Ganduje da APC sun shiryawa Kwankwaso wata sabuwar makarkashiya a Kano

Ganduje da APC sun shiryawa Kwankwaso wata sabuwar makarkashiya a Kano

Labarin da mu ke samu a halin yanzu shi ne an fara wani danyen shiri na janyo tsohon Gwamna Malam Ibrahim Shekarau cikin Jam’iyyar APC mai mulki bayan ficewar Rabiu Kwankwaso daga Jam'iyyar.

Ganduje da APC sun shiryawa Kwankwaso wata sabuwar makarkashiya a Kano
Jam’iyyar APC na yunkurin raba Shekarau da Kwankwaso a PDP

Jam’iyyar APC da kuma Gwamna Umar Abdullahi Ganduje sun fara kokarin maido Ibrahim Shekarau cikin Jam’iyyar da ya bari a 2014. Ganduje ya shirya wannan domin ganin an kyale tsohon Gwamna Kwankwaso a PDP.

Wasu manyan magoya bayan Shekarau sun bayyanawa Daily Trust cewa wasu daga cikin Gwamnatin Ganduje sun gana da su inda ake kokarin ganin sun bar PDP. Dama jiya mun ji cewa Ganduje ya leka wajen Shugaba Buhari.

Ba mamaki a samu matsala tsakanin Shekarau da ‘Yan Kwankwasiyya a Jam’iyyar PDP ta Jihar Kano don haka ne APC ke nema tayi amfani da wannan dama ta dauke Shekarau daga PDP. Shekarau yana cikin wadanda su ka kafa APC.

KU KARANTA: Ba na bukatar kujerar Sanata a 2019 inji Kwankwaso

Daya daga cikin ‘Yan gani-kashe-nin Shekarau watau Alhaji Muhammadu Inuwa Yusuf ya nuna cewa Mai gidan na sa na iya koma bangaren Gwamna Ganduje wanda yanzu sun samu matsala da tsohon Mai gidan sa da kuma Mataimakin sa.

Yanzu dai tsohon Kwamishinan Shekarau watau Salihu Sagir Takai yana neman Gwamna kuma yana da goyon bayan ‘Yan Kwankwasiyya. Idan har Shekarau ya bar PDP, an ragewa Kwankwaso da Jam’iyyar karfin gaske kafin zaben 2019.

Kun san cewa daga cikin ‘Yan Majalisar Wakilan da su ka bar APC su ka koma PDP akwai wasu mutum 10 daga Jihar Kano. ‘Yan Majalisar Tarayyan sun bi tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Kwankwaso ne zuwa inda su ka fito.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng