Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya

Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya danganta nasarar da daliban jihar Kaduna suka samu a gasar muhawar ta Duniya daya gudana a kasar Czech Republic a matsayin wata manuniya dake tabbatar da ingancin sauyin da gwamnatinsa ta kawo a shan’anin ilimi a jihar.

Daliban na jihar Kaduna sun sha gaban daliban kasar Amurka, Bulgaria, Slovenia da na kasar Slovakia, bayan sun sha karakaina a zagaye na kusa da karshe, inda suka daga martabar Najeriya ta zo na biyu a wannan gasa.

KU KARANTA: Maganganun da Kwankwao ya fada ma Buhari gaba da gaba a fadar shugaban kasa

Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya
Daliban

Jaridar Leadership ta ruwaito a yayin da gwamnan ya karbi bakoncin tawagar daliban a fadar gwamnatin jihar Kaduna yayi alkawarin gwamnati zata dauki nauyin karatunsu su shida gaba daya, sa’annan ya mika musu kyautar naira miliyan daya.

Cikin wata sanarwa da Kaakakin gwamnan, Samuel Aruwan ya fitar, ya bayyana manufar gwamna El-Rufai na cigaba da kokarin bayar da ingantaccen ilimi ga matasan jihar Kaduna, musamman duba da cewa dalibai biyar daga cikin tawagar dalibai ne a makaratun gwamnati.

Ruwa ba sa’an Kwando ba: Daliban Kaduna sun lallasa na kasar Amurka a gasar Duniya
Daliban

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sunayen daliban da makarantun da suka fito kamar haka; Mary Manuel Bawa, makarantar sakandari dake titin Independence Kaduna, Shuaibu Nura daga Alhudahuda Zaria, Auwal Abubakar daga makarantar Sakandari ta Kofar Kibo Zaria.

Sauran sun hada da Hauwa Mustapha daga makarantar sakandari ta Kofar Gaya Zaria, Joy Victor daga makarantar sakandarin cocin ECWA Kaduna sai Nathaniel Adamu daga sakandarin St John Kachia, daga karshe gwamnan ya yi alkawarin zai shirya ma daliban liyafar cin abinci don karramasu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng