Takara 2019: Yadda na kayar da Saraki da Kwankwaso zabe – Inji Atiku

Takara 2019: Yadda na kayar da Saraki da Kwankwaso zabe – Inji Atiku

Dan takarar kujerar shugaban kasa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yadda ya kada wasu gagga gagga yan siyasan Najeriya a wani zaben yanar gizo da wani fitaccen ma’abocin Twitter ya shirya, inji rahoton Daily Trust.

A wannan zabe na shugaban kasa da Japhet Omojuwa ya shirya, Atiku ya kayar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, Atiku ya samu kaso 42, yayin da Saraki ya samu kaso 37, sai Kwankwaso da ya zo na karshe da kaso 15 na kuri’un da aka kada.

KU KARANTA: Maganganun da Kwankwao ya fada ma Buhari gaba da gaba a fadar shugaban kasa

“Wannan zabe dai yazo ne a daidai lokacin da yan majalisa da dama suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC, don haka aka shiryashi don gwada kwarjinin sabbin yan siyasan da suka shigo PDP masu burin takarar shugaban kasa da na Atiku.” Inji ofishin yakin neman zaben Atiku.

Duk dayake Saraki bai fice daga APC ba, amma akwai rade radin yana nan tafe zuwa PDP, yayin da Kwankwaso ya koma PDP a ranar Talatar data gabata, kuma tambayar da aka yi masu zabe shine ‘Wanene zai zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP? Inda aka jero sunayen Bukola Saraki, Atiku Abubakar, Rabiu Kwankwaso da sauran.

A wani zaben makamancin wannan da Sanata Ben Murray Bruce ya shirya, Atikun ya sake lashewa, inda ya kada Buhari, Dankwambo da Tambuwa, ta hanyar samun kaso 44 na kuri’un, yayin da Buhari ya samu kaso 31, Dankwambo 17 sai Tambuwal mai 8.

Atikun yace: “Muna ta samun nasara a ire iren wannan zabe wanda sanannun masoya shugaba Buhari suke shiryawa don tantance goyon bayan shugaba Buhari bayan kwashe shekaru uku akan karagar mulki.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel