Ya kamata mu raba Gari da Saraki - Kakakin Jam'iyyar APC

Ya kamata mu raba Gari da Saraki - Kakakin Jam'iyyar APC

Mataimakin kakakin jam'iyyar APC, Yekini Nabena, yayi kira cikin gaggawa kan korar shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki daga jam'iyyar sakamakon gudanar da al'amurran dake cin karo da dokoki gami da tsare-tsare na jam'iyyar.

Nabena cikin wata sanarwa a ranar Larabar ta yau ya bayyana cewa, akwai sanya hannun Saraki tare da goyon bayan sa dangane da ficewar sanatoci 15 da kuma wasu mambobi na majalisar wakilai daga jam'iyyar a ranar Talatar da ta gabata.

Yake cewa, a sakamakon wannan kullaliya da Saraki ya jagoran ta na juyawa jam'iyyar sa baya, ko kadan ba ya da wani sauran hurumi na kasancewar sa cikin jam'iyyar a halin yanzu.

Duk da kasancewar shugabanni da sauran mambobi na jam'iyyar ba su da wani haufi ko mamaki dangane da ficewar wasu mambobin ta, sai dai al'amurran da Saraki ya gudanar tare da rawar da ya taka na goyon bayan hakan ya kamaci jam'iyyar ta rabi garin ta da shi.

Ya kamata mu raba Gari da Saraki - Kakakin Jam'iyyar APC

Ya kamata mu raba Gari da Saraki - Kakakin Jam'iyyar APC

Legit.ng ta fahimci cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne wasu jiga-jigan mambobin jam'iyyar suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun adawa musamman jam'iyyar PDP da ta kasance mafi shahara cikin su.

KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya nada sabon shugaban Ma'aikata na jihar Katsina

Kamar yadda Nabena ya bayyana, ko shakka babu alamu sun tabbatar da Saraki ya taka muhimmar rawa ta gani dangane da goyon bayan ficewar wasu mambobin jam'iyyar wanda hakan ya sabawa dokokin kowace jam'iyya ga ɗan cikin yayi adawa da ita.

A sanadiyar wannan fatali da dokokin jam'iyyar da al'amurran Saraki suka tabbatar, Nabena yake kira ga jam'iyyar ta aiwatar da raba hannun riga da shi domin Umma ta gaida Assha!

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel