Wani Limami ya saki matar sa bayan ta koma addinin Kiristanci

Wani Limami ya saki matar sa bayan ta koma addinin Kiristanci

A yau ne wata kotu dake zamanta a Igando ta jihar Legas ta raba auren wata mata, Rachael Olayiwola, da mijinta saboda sabanin addini.

Auren Rachael ya mutu ne bisa gazawarta wajen cika alkawarin da ta daukarwa mijinta cewar zata koma addininsa bayan sun yi aure.

Alkalin kotun, Mista Akin Akinniyi, y ace basu da wani zabi day a wuce a raba auren dake tsakanin Rachael da mijinta, Rabiu Olayiwola, bayan duk kokarin yi masu sulhu ya ci tura.

Tunda mai kara, Malam Rabi'u, ya kafe a kan raba auren shi da matarsa, Rachael, duk da an yi kokarin a sulhunta su amma a banza, kotu bata da wani zabi day a wuce ta raba auren,” a cewar alkali Akinniyi.

Wani Limami ya saki matar sa bayan ta koma addinin Kiristanci

Wani Limami ya saki matar sa bayan ta koma addinin Kiristanci

Yara 2 daga cikin ‘ya’ya 7 da ma’auratan suka haifa, zasu zabi wurin wanda zasu zauna tunda sun zama baligai," kamar yadda alkali Akinniyi ya fada.

Kazalika kotun ta umarci Malam Rabi’u da yake biyan tsohuwar matar tasa N25,000 kudin ciyarwa duk wata tare da umartarsa ya biya ta N350,000 domin ta nemi wurin da zata zauna.

DUBA WANNAN: Bana jin komai don na kashe mutum, maza hudu na kashe - Wata budurwa da bata rabuwa da Hijabi

Tun da farko, Malam Rabi’u, limami a wani masallaci, ya tunkari kotun ne da bukatar a raba auren shi da matarsa, Rachael, da suka shafe tsawon shekaru 21 suna tare bayan tayi ikirarin zama annabiya a coci duk da tayi masa alkawarin musulunta kafin su yi aure, kamar yadda kamfanbin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel