Ka rika kiyaye lafuzan ka - Ngige ya gargadi Oshiomhole

Ka rika kiyaye lafuzan ka - Ngige ya gargadi Oshiomhole

Ana cikin yanayi na jimamin rasa da yawa daga manyan jiga-jigan jam'iyyar APC da suka sauya sheka zuwa wasu jam'iyyun adawa a yau Talata, wani Ministan shugaban kasa Muhammadu Buhari na neman kai ruwa rana da shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole.

Kamar yadda shfin jaridar The Nation ya bayyana, Ministan kwadado da ayyuka, Sanata Chris Ngige, ya gargadi shugaban jam'iyyar Oshiomhole akan ya rika tauna magan tare da yiwa harshen sa linzami kafin ya furta.

Minista Ngige ya gargadi shugaban jam'iyyar su ta APC akan ya guji furta lafuza da ka iya janyo hargitsi tare da janyo mummunar fahimta gami da jefa shakku da kokwanto cikin zukatan al'ummar kasar nan sakamakon rashin zayyana masu tabbataccen zance.

Ka rika kiyaye lafuzan ka - Ngige ya gargadi Oshiomhole
Ka rika kiyaye lafuzan ka - Ngige ya gargadi Oshiomhole

Dan majalisar ta shugaban kasa cikin jawaban sa yayin ganawa da manema labarai ya bayyana fusatar sa dangane da kuskuren furuci na shugaban jam'iyyar da cewa, zantuka ne masu ɓatar da al'umma kasancewar su marasa tushe ko wani dalili.

Legit.ng ta fahimci cewa, Ngige ya fusata ne a sakamakon kuren zance da shugaban jam'iyyar ya bayyana dangane da kwangilar cibiyar inshora ta kasa, NSITF watau Nigeria Social Insurance Trust Fund.

KARANTA KUMA: Mutane 4 sun shiga hannu da laifin yiwa kamfanin MTN ɓarna

Oshiomhole karara ya bayyana cewa, Ministan ke da alhakin bayar da kwangila ga cibiyar ta NSITF da ya janyo tsaikon rantsar da shugabannin ta. Sai dai Ngige cikin fushi ya ce wannan zantuka ne na kage da shaci fadi.

Ngige ya kuma sake dora matashiyar zance domin tabbatar da gaskiyar lamarin da cewa, ko kadan kundin tsarin mulkin kasa bai yi tanadin wannan dama a gare sa ko ma'aikatar sa.

Bugu da kari, badakar zamba da cibiyar ta yi tsamo-tsamo a ciki ya sanya har ila yau ba a kaddamar tare da rantsar da jagororin ta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel