Jerin sunayen Sanatocin APC da suka rage bayan ficewar wasu 15
Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan, yace har yanzu APC ce ke da rinjaye a majalisar da sanatoci 52.
Mr Lawan ya bayyana hakan ne bayan wata taron jiga-jigan jam'iyyar APC da aka dauki sa'o'i biyu ana gudanarwa a yau Talata.
An fara taron ne bayan kammala zaman majalisar inda sanatoci 14 suka fice daga jam'iyyar APC, galibinsu suka koma babban jam'iyyar adawa ta PDP kamar yadda Premium Times ta wallafa.
Lawan yace APC ce ke da rinjaye da Sanatoci 52 yayin da mai biye mata PDP na da Sanatoci 50.
Mr Lawan ya fito da wata takarda inda ya lisafo sunayen sanatocin da ke cikin jam'iyyar na APC kamar haka:
Sanatocin sune; Adamu Aliero (Kebbi), Yahaya Abdullahi (Kebbi), Bala Ibn Na’Allah (Kebbi), Aliyu Wammako (Sokoto), Ibrahim Gobir (Sokoto), Ahmed Yerima (Zamfara), Kabir Marafa (Zamfara), Tijjani Kaura (Zamfara), Abu Ibrahim (Katsina), Umar Kurfi (Katsina), Kabir Gaya (Kano), Barau Jibrin (Kano), Abdullahi Gumel (Jigawa), Sabo Mohammed (Jigawa), Shehu Sani (Kaduna), Ahmed Lawan (Yobe), Bukar Abba Ibrahim (Yobe), Ali Ndume (Borno), Abu Kyari (Borno), Baba Kaka Garbai (Borno).
KU KARANTA: Zargin karkatar da kudade: EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa Ekweremadu
Saura sun hada da; Sabi Abdullahi (Niger), David Umar (Niger), Mustapha Muhammed (Niger), Abdullahi Adamu (Nasarawa), George Akume (Benue), Joshua Dariye (Plateau), Francis Alimikhena (Edo), Andrew Uchendu (Rivers), Magnus Abe (Rivers), Ovie Omo-Agege (Delta), John Enoh (Cross River), Nelson Effiong (Akwa Ibom), Andy Uba (Anambra), Sonni Ogbuoji (Ebonyi), Hope Uzodinma (Imo), Ben Uwajimogu (Imo), Danjuma Goje (Gombe), Binta Masi Garba (Adamawa), Ahmed Abubakar (Adamawa), Yusuf A. Yusuf (Taraba).
Har ila yau akwai; Oluremi Tinubu (Lagos), Gbenga Ashafa (Lagos), Solomon Adeola (Lagos), Tayo Alasoadura (Ondo), Gbolahan Dada (Ogun), Soji Akanbi (Oyo), Ajayi Boroffice (Ondo), Yele Omogunwa (Ondo), Abdulfatai Buhari (Oyo), Babajide Omoworare (Osun), Sola Adeyeye (Osun), Fatimat Raji-Rasaki (Ekiti).
Mr Lawan yace sanatocin na PDP ba za su kai 50 ba idan aka hada da wadanda aka kora daga jam'iyyar cikin kwanakin nan.
A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoton da PDP ta kori Sanata Buruji Kashamu a ranar Litini.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng