Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

Dan majalisar wakilai na jam'iyyar PDP mai wakilktan yankunan Oshodi/Isolo na jihar Legas kuma wanda ya jagoranci kudirin rage shakarun tsaya takara, Tony Nwulu, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa United Progressives Party (UPP).

Dan majalisar wanda aka haifa a jihar Imo ya bayyana cewa matakin ficewa daga PDP ne saboda yana son ya fito takarar gwamna a jihar Imo a shekarar 2019.

Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar
Tsalle-Tsallen 'yan siyasa: Wani dan majalisar PDP ya fice daga jam'iyyar

"Daga yau, na yi murabus daga matsayina a jam'iyyar PDP na koma UPP. Hakan ya yi dai-dai da sashi 86(g) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999).

KU KARANTA: Zargin karkatar da kudade: EFCC ta gayyaci mataimakin shugaban majalisa Ekweremadu

Nwulu yace ya dauki matakin ficewa daga jam'iyyar PDP ne bayan ya yi shawara kuma ya gano cewa jam'iyyar UPP ce kadai jam'iyyar da zata bawa matasa damar fitowa takara.

"Kamar yadda kuka sani, ina son fitowa takarar gwamna a jihar Imo a zaben shekarar 2019, kuma ina kyautata zaton UPP ce jam'iyyar da zata bani wannan damar," Kamar yadda Nwulu ya fadawa manema labarai.

Da aka masa tambaya ko akwai matsaloli a jam'iyyar ta PDP da ya fice, Nwulu ya amsa da cewa, "Dama tun farko akwai matsaloli a jam'iyyar PDP sai dai idan mutum baya son fada ma kansa gaskiya, kuma matsalolin ba za su taba karewa ba."

A wata rohoton, Legit.ng ta kawo muku labarin yadda aka tsige Kakakin majalisar jihar Benue na jam'iyyar APC. An tsige shi bayan majalisar ta gabatar da kudirin gazawa a kansa kuma mafi rinjayen 'yan majalisar suka goyi bayan sauke shi daga mukaminsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164