Ficewar Sanatoci 15 daga APC: Inai musu fatan Alheri – Inji Shugaba Muhammadu Buhari
Tun bayan sama da awanni biyar da shugaban majalisar Dattawa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya sanar da ficewar wasu gagga gaggan Sanatoci goma sha biyar daga jam’iyyar APC zuwa PDP, sai yanzu aka ji duriyar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Legit.ng ta ruwaito Shugaba Buhari yana yi ma wadanda suka fice fatan Alheri a gwagwarmayar siyasa, tare da jinjina ma shuwagabannin jam’iyyar APC da suka yi iya bakin kokarinsu na ganin sun hanasu ficewa.
KU KARANTA: Wani Sanata daga cikin Sanatoci 15 da suka fice daga APC ya karyata ficewarsa
Buhari ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter da yammacin ranar Talata, 24 ga watan Yuli, inda yace ya tabbata duk cikin wadanda suka fice babu wanda yake da matsala da shi ko gwamnatinsa, kuma ya girmama yancinsu na daukar duk matakin da ya dace dasu a siyasance.
“Ina yi ma yayan jam’iyyarmu da suka fice fatan Alheri. Na sani shugabancin jam’iyyar APC ta yi iya bakin kokarinta na ganin ta hanasu fita, amma abin ya ci tura, haka zalika ina kara jinjina ma shuwagabannin APC ta yadda suke kokari ba dare ba rana don ganin sun hada kan yayan jam’iyyar tare da shirya jam’iyyar ga samun nasara a zabukan dake tafe.” Inji Buhari
Daga karshe Buhari ya jaddada manufarsa ta yin aiki tare da dukkanin yan majalisa ba tare da la’akari da jam;iyyarsu, matukar zasu taimakeshi wajen ciyar da Najeriya gaba. Haka zalika ya kira ga magoya bayan APC da kada wannan ya damesu, kuma kada su karaya, saboda dama gabanin zabe lokaci na sauyin sheka.
A wani labarin kuma an bayyana sunayen Sanatocin da suka fice daga APC zuwa PDP kamar haka; Sen. Shaaba, Sen. Melaye, Sen. Shittu , Sen. Rafiu, Sen. Shehu Sani , Sen. Shitu Ubali, Sen. Isa Misau, Sen. Hunkuyi, Sen. Gemade, Sen. Danbaba,Sen. Nafada, Sen. Monsurat, Sen. Tejuoso, Sen. Nazif da Sen. Kwankwaso.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng