2019: Takara ta na nan daram – Shekarau

2019: Takara ta na nan daram – Shekarau

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan ilimi na kasa, Malam Ibrahim Shekarau, ya jaddada cewar babu gudu, babu ja da baya a burinsa na zama dan takarar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar PDP.

Shekarau ya bayyana haka ne ga manema labarai a birnin Owerri na jihar Imo inda ya halarci wani taron kaddamar da wani littafi.

Tsohon gwamnan ya nuna takaicinsa bisa halin da Najeriya ke ciki tare da bayyana cewar kasar na bukatar shugabanci mai ma’ana da zai kula da walwalar dukkan ‘yan kasa ba tare da nuna wariyar kabila ko addini ba.

2019: Takara ta na nan daram – Shekarau
Ibrahim Shekarau

Da yake kokawa a kan halin rashin tsaro a wasu sassan Najeriya, Shekarau ya bayyana cewar ko sau daya ba a samu barkewar wani rikici na kabilanci ko addini ba a tsawon shekaru 8 da ya yi yana mulkin jihar Kano.

DUBA WANNAN: Jerin sunayen 'yan majalisar wakilai da suka fice daga APC

Da yake bayyana yadda zai kawo karshen korafin da ‘yan kabilar Igbo ke yin a cewar ana mayar das u saniyar ware a Najeriya, tsohon gwamna Shekarau ya bayyana cewar ya yi bautar kasa ne a yankin kudu maso gabas na ‘yan kabilar ta Igbo sannan kuma ya shugabanci kungiyar shugabannin makarantun sakandire na kasa, a saboda haka yana da masaniyar matsalolin da yankin ke fama da ita kuma zai yi amfani da gogewarsa wajen warware masu dukkan matsalolinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel