Ministocin Jonathan da su ka samu karin girma bayan barin mulki

Ministocin Jonathan da su ka samu karin girma bayan barin mulki

A tsakiyar 2015 ne Gwamnatin Buhari ta karbi mulki daga hannun Jam’iyyar PDP. Bayan watanni 6 ne aka nada sababbin Ministoci. Sai dai daga cikin tsofaffin Ministocin Shugaban kasa Goodluck Jonathan akwai wadana gaba ta kai su.

Daga cikin Ministocin da yanzu su ka samu matsayi dabam-dabam a Duniya akwai:

Ministocin Jonathan da su ka samu karin girma bayan barin mulki
Ministar kudi a lokacin Shugaban kasa Goodluck Jonathan

1. Muhammad Pate

Tsohon Ministan lafiya a Gwamnatin Jonathan watau Dr. Muhammad Ali Pate yanzu babban Malami ne a Jami’ar Duke. Tun a 2013 Dr. Pate ya ajiye aikin sa ya tafi Kasar waje. Pate yayi karatu ne a Jami’ar ABU Zaria da wata Jami'a a Landan.

KU KARANTA: Oshiomhole yayi barazanar dakatar da Ngige daga APC

2. Akinwumi Adesina

Dr. Akinwumi Adesina wanda tsohon Ministan gona ne a Najeriya ya zama Shugaban babban bankin nan na AfDB na cigaan Afrika. A lokacin Shugaba Muhammad Buhari ne tsohon Ministan Kasar ya samu wannan babban mukami.

3. Ngozi Iweala

Tsohuwar Ministar kudin Kasar watau Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta samu mukamai iri-iri bayan ta bar Gwamnati. Kwanan nan ne ma Kamfanin sadarwar nan na Tuwita ta nada Okonjo-Iweala a cikin manyan Darektocin ta na Duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel