An kashe wani babban Soja da ‘Dan Sanda bayan an sace mutane da dama a hanyar Abuja
- Mun samu labari cewa ansace mutane da dama a kan yar Abuja a jiya
- Masu garkuwa da mutane sun tsare hanyar Garin Kaduna zuwa Abuja
- Daga cikin wadanda aka kashe har da wani Soja da kuma ‘Dan Sanda
Mun samu labari daga Daily Nigerian cewa masu garkuwa da mutane sun kuma yin wata barna a makon nan inda su ka kashe wani babban Jami’in Soja sannan kuma su ka sace Bayin Allah rututu.
Jaridar ta bayyana cewa wasu masu garkuwa da mutane kimanin mutum 10 ne su ka tare hanyar Abuja zuwa Kaduna a jiya Ranar Lahadi inda su ka sace mutane da-dama. An yi kusan sa’a guda ana wannan ta’adi bayan faduwar rana.
KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi arangama da 'Yan Boko Haram
An yi wannan barna ne a wani Kauye da ake kira Gidan busa. Wannan kauye yana tsakanin Garin Kere da Kateri a kan babban titin Kaduna zuwa babban Birnin Tarayya Abuja. Jaridar tace an fara wannan abu ne bayan karfe 6 na yamma.
Majiyar ta bayyana cewa daga cikin wadanda aka ga bayan su har da wani ‘Dan Sanda da wani Jami’in Soja da yake tafiya da ‘Yar sa da kuma Dogari. Nan take dai aka kash Sojan da Iyalin sa yayin da aka yi Dogarin rauni ya tsere.
Jami’an tsaro dai ba su iya yin komai ba ko da su ka samu labari inda su ka ce su na jiran a aiko karin mutanen su. Dama jiya kun ji cewa mutane su na kokawa a kan yadda harkar tsaro ya sukurkuce baki daya musamman a Kaduna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng