Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

A yau ne jirgin farko na maniyyata aikin Hajjin bana daga Najeriya suka isa birnin Madina na kasa mai tsarki.

A jiya, Asabar, ne hukumar jin dadin alhazai ta kasa (NAHCON) ta sanar da fara jigilar maniyyata aikin Hajji na bana.

Hukumar ta NAHCON ta sanar da hakan da yammacin ranar Juma'a tare da bayyana cewar ta kammala shiri tsaf domin fara aikin jigilar maniyyatan.

Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

Wakilan hukumar NAHCON bayan saukar su a Madina

Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

Jirgin farko na Alhazan Najeriya

Tuni kasar Saudiyya ta fara gudanar da shirye-shiryen fara karbar bakin alhazai da zasu yi aikin Hajjin bana.

Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Usara, ta bayyana cewar za a fara jigilar ne ranar Asabar da alhazan jihar Kogi a filin jiragen sama na kasa da kasa dake Abuja da misalin karfe 11:00 na safe.

Saidai bisa ga alamu hakan bata samu ba, domin sai yau, Lahadi, jirgin farko ya sauka birnin Madina da maniyyata na farko da suka tashi daga Najeriya.

DUBA WANNAN: Gwamna Bello ya tonawa Dino Melaye asiri a kan kone ajuzuwan da ya gina

Kazalika ta sanar da cewar za a fara jigilar maniyyatan na jihar Kogi ne a jirgin saman kamfanin MAX Air da zai dauke su kai tsaye zuwa Madina.

Fatima ta shawarci alhazan da su kasance masu hakuri da irin jerin tantancewa da kasar Saudiyya ke yiwa baki da zasu shiga kasar tare da bukatar su zama wakilan Najeriya nagari yayin gudanar da ibadar aikin Hajji.

Hajjin Bana: Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina, duba hotuna

Jirgin farko na Alhazan Najeriya ya sauka birnin Madina

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel