Tsananin matsa ya sanya wani tsoho shekawa lahira a hannun jami’an SARS a Kano
- Cinikin layar zana yazo da matsala har anyi asarar rai
- Sai dai kuma mutuwar ta zo da wani yanayi mai cike da sarkakiya, domin kuwa wanda ya siyar da layar ya mutu ne a hannun 'yan sanda
- Yanzu haka dai iyalan mamacin sun bukaci ba'asin yadda akai mahaifin nasu ya sheka lahira bayan sun tabbatar da lafiyarsa kalau
Wani malami mai suna Musa Ardo mai shekaru 70 ya gamu da ajalinsa a hannun jami'an ‘yan sanda na SARS.
Al'amarin ya samo asali ne a dalilin sayar wa wani mutum mai suna Alhaji Musa layar bata.
Alhaji Musan ya je kauyen Gedege dake karamar hukumar Kubau dake jihar Kaduna domin samun layar batan ne a wajen Musa Ardo don kariya.
Suka tsadance akan kudi Naira dubu 30,000 tare da bashi tsauraran sharudda saboda gujewa bacewar layar baki daya.
Cikin yan kwanaki AlhAji Musa ya dawo wajen mamacin yana mai shaida masa cewa layar ta bata, sannan ya bukaci a bashi wata, wanda hakan bai zaunawa mamacin ba don a ganinsa yaudararsa za’ai.
Nan take ya bukaci ya dawo masa da layar da ya ba shi tunda farko kafin ya ba shi wata ko kudinsa. Kamar yadda Daily Nigerian ta rawaito.
Bayan kwanaki biyu sai ga Alhaji Musa ya sake dawowa, a wannan karon da jami'an ‘yan sanda na SARS daga Kano, yana mai ikirarin cewa sun tsadance akan zai masa aikin layar akan kudi Naira miliyan 2 wanda daga bisani suka amince akan miliyan 1.6, wanda marigayin ya musanta wannan zargi na cewar ya karbi wadannan makudan kudade.
A cikin wata takardar korafi ta lauyan dake karkashin Al Qasim Ja'afar and co. (Gidado chambers) ya aike ga shugaban hukumar ‘yan sanda na jihar Kano, cewa iyalan mamacin sun bukaci jami’an na SARS da su yi bayani game da irin azabar da suka ganawa mamacin tare da bayar da rahoton yadda akai ya mutu.
KU KARANTA: Ayya: wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers
Daya daga cikin 'ya'yan mamacin ya bayyana cewa "Kwana daya da kama mahaifinmu muka bisu zuwa Kano a lokacin lafiyarsa kalau, amma bayan kwana biyu sai aka kira mu cewa mu zo kano ofishin SARS domin mahaifinmu yana cikin wani hali.
Ko da muka je Kano sai muka iske cewar ya rasu har sun kai gawarsa dakin ajiye gawarwaki na asibitin Murtala Mohammed dake Kano".
Majiyarmu dai ta tabbatar da cewa wanda ya sayi layar batar ya bayyana bacin ransa yayinda aka kira shi a waya domin jin ta bakinsa game da bacewar layar, sai ya rika cewa “A ina ka samu lamba ta”.
Kakakin hukumar yan sanda na jihar Kano Magaji Musa Majiya yayi karin haske game da rasuwar mamacin, inda yace mamacin ya fara rashin lafiya ne mai kama da ta kwalara, inda aka kaisa asibitin Sir Sanusi dake kan titin Hadeja kafin daga bisani a maida shi asibitin koyarwa na Murtala Mohammed, wanda a nan ne ya ce ga garin ku nan.
Dama dai jami'an SARS sun yi kaurin suna wajen aikata laifukan da suke na cin zarafi, sauka daga layi da kuma shiga gonar da ba ta su ba, hakan har tasa a baya akai ta kiraye-kiraye don ganin an soke su, amma hakan bai tabbata ba, kasancewar suna bayar da gagarumar gudunmawa wajen dakile manyan laifuka wanda dama don shi aka yi su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng