Cikin hoto: An yi mummunan hatsarin mota tsakanin motar Dangote da ta fasinjoji, da dama sun mutu
A yammacin yau, Asabar, ne aka samu afkuwar wani mummunan hatsarin mota a kan jihar Nasarawa zuwa garin Jos.
Hatsarin ya afku ne a garin Akwanga tsakanin kwalejin Ilimi da makarantar sakandire ta Mada Hill.
Rahotanni sun bayyana cewar motar fasinja ta jihar Gombe ce tayi taho mu gama da motar kamfanin Dangote kuma nan take mutane 8 suka mutu.
DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun harbe babban limami a jihar Filato
Wani shaidar gani da ido y ace mai yiwuwa adadin mutanen da suka mutu ya karu, musamman ganin yadda wasu fasinjojin ke cikin mawuyacin hali. Duba hotunan;
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng