Uwargida ta dawo da N50,000 na sadakinta don a raba ta da mijinta, bayan ya more ta shekaru takwas

Uwargida ta dawo da N50,000 na sadakinta don a raba ta da mijinta, bayan ya more ta shekaru takwas

- Uwar gida na son dawo da sadaki don a raba aurenta na shekaru 8

- Duk da mijin ya more ta, a shari'ance sai ta dawo da sadakin don ya kara sabon aure

- A yanzu kotun Magajin Gari a Kaduna ta Shari'ar Islama ke sauraron karar

Uwargida ta dawo da N50,000 na sadakinta don a raba ta da mijinta, bayan ya more ta shekaru takwas
Uwargida ta dawo da N50,000 na sadakinta don a raba ta da mijinta, bayan ya more ta shekaru takwas

Malama Hanifa Adamu, matar auren shekaru takwas, ta roki kotu da ta raba aurenta saboda gajiya da zaman auren da tayi, a jihar Kaduna gaban kotun shari'a dake Magajin Gari. Ta kuma tabbatar a shirye take ta dawo da sadakinsa kamar yadda shariar Islama ta tanada.

Lauyanta, Barrister Junaidu Aminu, ya karanto jawabinta kamar haka: "Ya mai shari'a, na gaji da auren mijina da aka daura mana a 2010, kuma shirye nake na biya shi N50,000 saboda bazan iya biyaa masa bukatunsa ba a matsayina na matar sa."

DUBA WANNAN: Sanatoci 21 masu niyyar sauyin sheqa

Lauyan wanda ake kara dai, watau Ibrahim Isyaku wanda yana can jihar Pilato yaje aiki, ya kare maigidan nasa da cewa kotun ta shari'a, batta da hurumin sauraron karar, kuma yana bukatar tattaunawa da mijin, don haka a basu lokaci.

Lauyan, Barrister Badammasi yayi nasarar samun dage sauraron bahasinsu zuwa watan 15, Agusta don ci gaba da shari'ar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng