Kashe-kashe a Zamfara: Marafa ya yiwa gwamna Yari ta-tas a kan tafiya zabe jihar Osun

Kashe-kashe a Zamfara: Marafa ya yiwa gwamna Yari ta-tas a kan tafiya zabe jihar Osun

Sanata mai wakiltan mazabar Zamfara Central, Kabiru Marafa, ya cacaki gwamna Abdulaziz yari na jihar Zamfara saboda tafiyar da ya yi sa ido a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC a jihar osun alhalin ana cigaba da kashe mutane a jiharsa.

A wata sako da ya fitar a ranar Juma'a, Marafa ya kuma zargi Kwamitin gudanarwa na APC karkashin jagorancin shugabanta, Adams Oshiomole, da rashin adalci ga al'ummar Zamfara saboda aika Yari zuwa jihar Osun.

Sanatan yace ya yi mamakin ganin hotunan gwamna Yari a jihar Osun yayin da yake shirye-shiryen fara gudanar da zaben fidda gwanin wadda Kwamitin gudanarwa na APC ta daura masa nauyin gudanarwa.

Sanata Marafa ya sake cacakar gwamna Yari a kan kashe-kashen Zamfara
Sanata Marafa ya sake cacakar gwamna Yari a kan kashe-kashen Zamfara

DUBA WANNAN: Dattijan Arewa sun fiye son kansu, kunya ce ta ishe su suke so su tade kafar Buhari - Fadar shugaban kasa

"A tunani na, Jam'iyyar APC karkashin jagorancin Oshiomole ba ta yiwa mutanen Zamfara Adalci ba domin sun san mutanen jihar na bukatar gwamnan su saboda halin da suke ciki amma aka tura shi jihar Osun.

"Ta yaya gwamnan da 'yan baranda ke kashe mutane a jiharsa zai rika yawo a Najeriya da sunan yiwa kasa hidima?

Marafa yace babu yadda za'ayi gwamnan da ya gaza samar da tsare-tsare da zai kare lafiya da dukiyoyin al'ummarsa ya tafi ya gudanar da zaben fidda gwani a Osun ba tare da matsala ba.

Ya kara da cewa, "Ya kamata a sanar da gwamnan cewa jihar Zamfara ce ma mazabarsa ta farko kuma idan ba zauna ya tsara yadda zai samar da tsaro a jiharsa ba, zai cigaba da rudar kansa ne kawai.

"Ana zubda jinin al'umma a Zamfara kuma har yanzu bamu ga wata hubbasa daga gwamnatin Yari ba don ganin an kawo karshen matsalar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164