Jerin Shugabannin Kasashen da su kayi shekara da shekaru su na mulki
A Afrika dai a kan samu shugabanni su dade su na mulki, wasu ma har ta kai su daura ‘Ya ‘yan su. Yanzu mun kawo maku jerin wadanda su ka fi kowane dadewa a kan karaga ganin cewa Paul Biya na neman zarcewa kan kujerar sa a Kamaru.
1. Shugaban Kasar Guinea
Shugaba Teodoro Obiang Nguema na Kasar Equatorial Guinea ya shafe shekara 39 yana mulkin Kasar sa. Teodoro Nguema ya hau mulki ne a shekarar 1979 lokacin yana Matashi. Yanzu yana wa’adin sa na 7.
KU KARANTA: Ashe cikin Kakannin Barack Obama akwai Musulmai?
2. Shugaban Kasar Kamaru
A halin yanzu bayan Teodoro Obiang Nguema babu Shugaban kasar da ya kai Paul Biya na Kasar Kamaru dadewa a kan mulki. Biya yayi shekara 35 yana mulkin Kasar Kamaru kuma yana sa ran zarcewa bana.
3. Shugaban Kasar Kongo
Denis Sassou Nguesso yayi shekaru 34 a kan karagar mulkin Kasar Kongo idan aka hada wa’adin da yayi. Da farko Sassou Nguesso yayi mulki a 1979 har zuwa 1992. Bayan an gama yaki a kasar kuma ya kara dawowa kujerar a a 1997.
Bayan nan kuma akwai irin su Shugaba Yoweri Museveni na Uganda wanda yayi shekaru 32 yana mulki. A Kasar Sudan ma kuwa Shugaba Omar Al-Bashir ya shafe shekara 29 yana kan karaga. A nan kusa Chad Idriss Deby ya hau mulki ne tun 1990.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng