Muna bukatar ka a APC, karka gudu - Shugaba Buhari ya roki Bukola Saraki
- Ana zargin su Bukola Saraki ke son yaga jam'iyyar APC
- Shugaba Buhari a baya ya bari a yankwana na ukun a kasar nan
- Yanzu dai kotu ta wanke shi, don haka watakil a tafi tare
Daga cikin kokarin sulhun da ake cikin masu kokarin sai sun yaga jam'iyya, ana ganin su Bukola Saraki, wadanda aka bari hukumomi daban-daban ke yankwanawa, su suke daukar nauyinsu a kokarinsu na barin jam'iyyar tare da kujerunsu.
Sai bayan an yaga jam'iyya ne ake iya samun wadanda zasu barta daga cikin 'yan majalisu, kamar yadda yake a tsarin mulkin kasar nan. Kuma dama hakan ne ya bada damar sauyin shekar wasu daga cikinsu a zagayen zabukan 2015.
DUBA WANNAN: Jirgin kasa ya nike Mutane a mota
A ganawarsu ta daren jiya a fadar Aso Rock, shugaba Buhari, da mataiimakinsa, da ma shugaban jam'iyya sun shawo kan Bukola Saraki, kan batun barazanarsu ta barin jam'iyyar APC daga barakar r-APC.
PDP dai kan ganawar sirri da wadannan jam'iyyu jiga-jigai masu iya kawowa APC tangarda.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng