Kashi na biyu na N-Power wanda za'a ara nan da mako daya zai dauki mutum 300,000

Kashi na biyu na N-Power wanda za'a ara nan da mako daya zai dauki mutum 300,000

- Gwamnatin tarayya ta kammala shirye shiryen samar da gurbin mutane 300,000 don su amfana da N-Power kashi na biyu wanda zai fara daga 1 ga watan Augusta

- Babban mataimakin shugaban kasa na musamman akan yada labarai, Mista Laolu Akande ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis

- Akande ya bayyana cewa akwai mutane 200,000 dake amfana da shirin, mutane 500,000 ne zai zama jimillar wadanda zasu amfana da shirin na da watan Augusta

Kashi na biyu na N-Power wanda za'a ara nan da mako daya zai dauki mutum 300,000
Kashi na biyu na N-Power wanda za'a ara nan da mako daya zai dauki mutum 300,000

Gwamnatin tarayya ta kammala shirye shiryen samar da gurbin mutane 300,000 don su amfana da N-Power kashi na biyu wanda zai fara daga 1 ga watan Augusta.

Babban mataimakin shugaban kasa na musamman akan yada labarai, Mista Laolu Akande ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis.

Akande ya bayyana cewa akwai mutane 200,000 dake amfana da shirin, mutane 500,000 ne zai zama jimillar wadanda zasu amfana da shirin na da watan Augusta.

Yace an kirkiro da N-Power din ne don ta amfani yan Najeriya ba tare da dubi ga yare ko addini ba a fadin jihohi 36 na kasar nan.

DUBA WANNAN:

Akande yace tare da hadin guiwar mashiryan shirin a duk fadin jihohi, sababbin diban za a watsa su zuwa inda ya dace kafin lokacin da zasu fara aikin.

Yace jerin sunayen na kowacce jiha zuwa kananan hukumomi zai fito ne a ranar juma'a, 20 ga watan yuli, 2018.

Duk wadanda suka samu damar shiga shirin a shirin N-Power kashi na biyu zasu yi aiki ne na shekara 2, farawa 1 ga watan Augusta 2018 zuwa 31 ga watan yuli, 2020.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng