Jinin da ake zubarwa a Najeriya ya yiwa - Sarkin muslmi ya koka

Jinin da ake zubarwa a Najeriya ya yiwa - Sarkin muslmi ya koka

Sarkin musulmi kuma shugaban kwamitin koli ta harkokin addinin musulunci (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya koka kan yadda ake zubda jinin al'umma a kasar, inda yace ana kara samun karuwar fashi da makami da ta'addanci.

Kazalika, Basaraken Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi shima ya yi korafi kan yadda 'yan siyasa ke amfani da kudi wajen cinma burinsu da kuma irin matsalar da hakan ke haifarwa kasar.

Shugabanin biyu sunyi jawabi ne a wata taron masu ruwa da tsaki a kungiyar matasa ta Youths off The Street Foundation tare da hadin gwiwar Cibiyar hadin kan addinai ta Najeriya ta kafa don kaddamar da gangaminta na yaki da magudin zabe.

Jinin da ake zubarwa a Najeriya ya yiwa - Sarkin muslmi ya koka

Jinin da ake zubarwa a Najeriya ya yiwa - Sarkin muslmi ya koka

DUBA WANNAN: Wasu 'yan bindiga sun kashe wani dan acaba haka siddan a Ibadan

Sultan yace ba zai yiwu yan Najeriya su cigaba da kashe junansu da zubda jini ba da sunan addini saboda dukkan addinan musulunci da Kirista bai amince da kashe rayyuka ba.

A cewar Sultan, "A matsayinmu na Musulmi da Kirista, mun san darrajar rai. Ba zai yiwu mu riga kashe mutanen da basu san hawa ko sauka ba da sunnan addini. Wannan ba dai-dai bane, dole mu tsawata kuma mu kawar dashi daga cikin al'ummar mu. Dole mu hada kai wajen magance masu wannan aika-aikar.

"Ana zubja jinin mutane da yawa a Najeriya, mutanen da kuma babu ruwan su. Wannan abin yana faruwa a sassan da yawa na Najeriya, kuma idan bamu dauki mataki kan lamarin ba, ba zamu samu zaman lafiya ba, kuma idan babu zaman lafiya, baza mu samu cigaba ba.

"Ya zama dole 'yan Najeriya su farga mu hada kai waje guda saboda addinan mu basu amince mu rika kashe juna ba. Addinan mu sun koyar damu zaman lafiya ne da kuma kaunar juna. Saboda haka, ni ban san inda wasu mutane ke da'awar kiyaya da kashe mutane ba."

Shima shugaban kungiyar Kirista ta Najeriya CAN ya yi jawabi inda ya bukaci al'umma su zauna lafiya da juna. Ya kuma yi kira ga 'yan siyasa su dena daukan siyasa da zafi domin ba zai mutum ya rike matsayin siyasa zai iya taimaka wa al'umma ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel