Da duminsa: Ana can an saka labule tsakanin Osinbajo, Saraki da wadansu gwamnoni 5

Da duminsa: Ana can an saka labule tsakanin Osinbajo, Saraki da wadansu gwamnoni 5

An shiga wata ganawar sirri a gaggauce tsakanin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu gwamnoni.

Rahotanni dake shigowa dakin buga labarai na Legit.ng sun tabbatar mana da cewar, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da wasu gwamnoni na can suna wata ganawar sirri a ofishin shugaban kasa dake fadar gwamnatin Najeriya.

Da duminsa: Ana can an saka labule tsakanin Osinbajo, Saraki da wadansu gwamnoni 5

Saraki da Osinbajo

Gwamnonin da aka hango wurin taron sun hada da na jihar Katsina, Amina Bello Masari, na Zamfara, Abdulaziz Yari, na jihar Kebbi, Atiku Bagudu, na jihar Ogun, Ibikunle Amosun da kuma sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.

DUBA WANNAN: Buhari ya tura sunayen wasu 'yan arewa 2 majalisa domin tabbatar da su a manyan mukamai

Saidai tunu shugaba Buhari ya fita daga ofishin nasa kafin karasowar Saraki da gwamnonin, sannan ba a bayyana ajendar taron bag a kowa.

A yau ne dai aka samu yamutsi a majalisar dattijai bayan shugaba Buhari ya bukaci ‘yan majalisar su cire dukkan aiyukan da suka saka a cikin kasafin kudin bana domin samun kudin da za a bawa hukumar zabe da zata yi amfani das u domin shirya zabukan shekarar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel