Da nayi masa biyayya gara na biya shi N50,000 kudin sadakin da ya biya – Wata mata ta sanar da kotun musulunci
- Wata matar aure ta gurfanar da mijinta a gaban wata kotun shari’ar musulunci dake Magajin Gari a Kaduna, tana mai neman ya sawwake mata
- Lauyan dake kare matar ya shaidawa kotu cewar wacce yake karewa na bukatar a raba aurensu da mijinta saboda ba zata iya yi masa biyayya ba
- Alkalin kotun, Dahiru Lawan, ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 15 ga watan Agusta domin bawa wanda ake kara dammar bayyana a gaban kotu
Wata matar aure, Hanifa Adamu, ta gurfanar da mijinta, Ibrahim Adamu, a gaban wata kotun shari’ar musulunci dake Magajin Gari a Kaduna, tana mai neman ya sawwake mata.
Lauyan dake kare Hanifa, Junaidu Adamu, ya shaidawa kotu cewar wacce yake karewa na bukatar a raba aurensu da mijinta saboda ba zata iya yi masa biyayya ba.
“Wacce nake karewa a shirye take ta dawo da N50,000 da ta karba a matsayin sadaki daga hannun mijinta domin ya sawwake mata,” lauya Junaidu ya sanar da kotu.
Saidai, Badamasi Adam, lauyan dake kare wanda ake kara ya nuna shakku bisa ikon kotun na sauraron karar tare da bayyana cewar wanda yake karewa yanzu haka yana kasar saudiyya. Kazalika ya bukaci a bas hi lokaci domin gabatar da hujjojin cewar kotun bat a da hurumin sauraron karar da aka shigar gabanta.
DUBA WANNAN: 'Yan sandan tawagar Osinbajo sun tara wa jami'an kwastam gajiya a jihar Katsina
Bayan ya kamala sauraron kowanne bangare, alkalin kotun, Dahiru Lawan, ya daga sauraron karar ya zuwa ranar 15 ga watan Agusta domin bawa wanda ake kara dammar bayyana a gaban kotu, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng