Ba zan iya ba: Wani Saurayi ya rabu da Budurwar sa saboda ‘dan karen kazantar ta

Ba zan iya ba: Wani Saurayi ya rabu da Budurwar sa saboda ‘dan karen kazantar ta

- Wani Matashi ya rabu da Budurwar sa saboda ta cika kazanta

- Wannan saurayi yace sam Budurwar ta sa ba ta wanke kayan ta

- Hakan ya sa ya tona mata asiri kuma su ka raba Jiha don ya huta

Wani irin labari mai ban mamaki ya zo mana kwanan nan inda wani Saurayi ya rabu da Budurwar sa da su ka dade tare saboda ta cika mugun kazanta duk da irin shawarwarin da ya rika ba ta.

Ba zan iya ba: Wani Saurayi ya rabu da Budurwar sa saboda ‘dan karen kazantar ta
Saurayi da Budurwar sun rabu saboda ba ta sukola

Daniel Ogbeide wani Matashi ne a Najeriya wanda ya fito har shafin sa na sadarwa na zamani na Facebook a gaban Duniya ya tonawa Budurwar sa asiri. Ogbeide yace Budurwar ta sa ta cika kazanta har ta kai ba ta wanke ‘dan banten ta.

KU KARANTA: Ana neman sayen ‘Dan kwallon Najeriya Ahmed Musa ruwa-a-jallo

Wannan Saurayi ya tonawa Budurwar ta sa asiri ne da nufin ko ta canza halin ta na mugun kazanta. Ogbeide sai da ya nuna hotunan kayan wannan Budurwa cikin mugun dauda, wanda daga ciki har da banten ta da yayi baki saboda kazanta.

Shi dai wannan Bawan Allah mai suna Daniel Ogbeide yace daga yanzu fa babu shi, babu wannan yarinya ganin kuwa cewa ta ki canza halin ta na zaman dauda, duk da irin jan kunnen ta da yayi. Yace sau da dama shi yake wanke mata kaya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng