Wasu 'yan bindiga sun kashe wani dan acaba haka siddan a Ibadan
A yau Alhamis ne wasu 'yan bindiga da ba'a gano ko su waye ba suka harbe wani dan acaba har lahira a layin asibitin Adeoyo dake unguwar Fodasis dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Jami'in kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) da ya ziyarci inda aka yi harbi yace ya tarar da gawar dan acabar a kwance a gefen titi.
NAN ta ruwaito cewa 'yan bindigan sun harbi mutumin ne a kirjinsa misalin karfe 5.40 na asuba bayan sun kwace babur dinsa.
DUBA WANNAN: An yankewa wata hukuncin daurin shekaru 3 bayan ta yiwa wata kaca-kaca da reza
Wani wanda abin ya faru a idanunsa da ya nemi a sakayya sunansa ya fadawa majiyar Legit.ng cewa 'yan bindigan sun fara tafiya bayan kwace babur din amma suka dawo suka kashe mutumin saboda ya fara ihu yana son tona musu asiri.
"Ina tunanin mutumin da dan acaba bane saboda irin tufafin da ya sanya. Ba mamaki yana hanyarsa ta zuwa wajen aiki ne," inji ganau din.
NAN ta ruwaito cewa daga bisani jami'an 'yan sanda sun dauke gawar zuwa dakin ajiye gawarwaki na asibitin Adeoyo.
A lokacin da aka tuntubi Kakakin hukumar yan sanda na jihar, SP Adekunle Ajisebutu, ya shaida wa NAN cewa har yanzu ba'a sanar dashi labarin afkuwar lamarin ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng