Duk irin mukamin da Buhari zai baiwa Rarara ba zai tara abinda na tara ba – Inji Nazir Ahmad

Duk irin mukamin da Buhari zai baiwa Rarara ba zai tara abinda na tara ba – Inji Nazir Ahmad

Zo mu zauna, zo mu saba, wani karin magana na Malam Bahaushe, kuma dama ai ko a tsakanin harce da hakori ana samun sabani, don kuwa anan ma wata sabuwatr bahallatsa ne ya barke a tsakanin wasu fitattun mawakan Kannywood.

Jarida Rariya ya ruwaito shahararren mawakinnan da ake yi ma lakabi da Sarkin waka, wato Nazir Ahmad yana mayar da martani ga labarin da ake yadawa na cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada mashahurin mawakin nan, Dauda Kahutu Rarara mukamin shugaban mawakan Buhari na yakin neman zaben 2019.

KU KARANTA: An zo wajen: Za’a fara biyan sabbin yan N-Power albashinsu daga watan Agusta

Majiyar Legit.ng ta ruwaito magoya baya na rade radin wai Naziru na hassada da wannan cigaba da Rarara ya samu, da wannan ne Nazirun yace ko da Rarara zai kwashe shekaru dari akan wannan mukami da Buhari nada shi ba zai taba tara abinda ya mallaka ba.

Duk irin mukamin da Buhari zai baiwa Rarara ba zai tara abinda na tara ba – Inji Nazir Ahmad
Nazir da Rarara

A satin data gabata ne fadar shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya dake bayyana an nada Rarara daraktan wakokin yakin neman zaben shugaba Buhari a zaben 2019.

Sanarwar ta kara da bayyana sunayen mutanen dake cikin wannan kwamiti da zasu yi aiki tare da Rarara da suka hada da fitaccen dan fim din Turanci na Najeriya kuma dan majalisa a majalisar dokokin jihar legas Desmond Elliot a matsayin Kaakaki, sai kuma shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Imo, Uche Uwgumba Nwosu a matsayin sakatare.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng