Ko kun san yawan hanyoyin da gwamnatin tarayya tayi daga shekarar data wuce zuwa yanzu
A ranar Alhamis dinnan ne hukumar kula da titunan gwamnatin tarayya (FERMA) tace an kammala sama da aiyukan manyan tituna guda 88 da aka saka a kasafin kudin shekarar 2017
A ranar Alhamis dinnan ne hukumar kula da titunan gwamnatin tarayya (FERMA) tace an kammala sama da aiyukan manyan tituna guda 88 da aka saka a kasafin kudin shekarar 2017.
Shugaban bangaren sadarwa da hulda da jama'a, Mrs Maryam Sanusi, ta tabbatar da hakan a wata tataunawa da tayi da manema labarai a Abuja.
DUBA WANNAN: EFCC zata hada karfi da karfe da kasar Ingila wurin kawo karshen cin hanci a Najeriya
Sanusi tace wasu aiyukan tituna 66 da suke a kasafin kudin 2017, anyi kashi 50 a kansu.
Ta lissafo wasu daga cikin kammalallun aiyukan, sun hada da :
Gyaran titin Biu-WanDali dake jihar Borno, babbar hanyar Garkida-Gombi ta Adamawa da gyaran titunan Ningi dake jihar Bauchi.
Gyaran titin tarayya na Awe-Iwo dake jihar Oyo, titin Benin-Abraka dake Edo, titin daga Iyah-Obelle a Kogi, gyaran titin Ribah-Diri-Rijau dake jihar Kebbi da sauransu.
Sanusi tace hukumar su zata tabbatar da kammaluwar duk aiyukan da aka fara.
"Tabbacin shine in dai akwai isassun kudi, hukumar zata tabbatar da an kammala aiyukan."
Kamar yanda tace, wadannan titunan suna taka rawa wurin habaka tattalin arziki da siyasar kasar nan. Sanusi tayi kira ga yan Najeriya dasu gane cewa tituna kadarori ne, muna amfani dasu gurin zuwa aiyukan mu na yau da kullum. Don haka ayi amfani dasu yanda ya dace.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng