Rayuka 3 sun salwanta, Mutane 4 sun jikkata cikin wani mummunan hatsari a jihar Ogun
Afkuwar wani hatsarin mota ta yi matukar muni yayin da rayukan mutane uku suka salwanta da jikkatar wasu hudu a babbar hanyar Baagban dake birnin Abeokuta a ranar Larabar da ta gabata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, afkuwar hatsarin ta hadar da wata karamar mota kirar Toyota Corolla da wata Motar haya kirar Micra kan babbar hanyar Abeokuta zuwa Ibadan.
Kakakin hukumar kula da manyan hanyoyi Mista Babatunde Akinbiyi, shine ya bayar da tabbacin wannan lamari yayin ganawa da manema labarai da cewar hatsarin ya ritsa da mutane bakwai inda uku suka riga mu gidan gaskiya a babban birnin na Abeokuta.
Legit.ng ta fahimci cewa, afkuwar wannan hatsari ta ritsa da mutane bakwai da suka hadar da maza biyar da mata biyu.
KARANTA KUMA: Wani 'Dan shekara 52 ya zakkewa wani Matashi mai shekara 14 ta Dubura a jihar Legas
Akinbiyi ya bayyana cewa, hatsarin ya afku ne a sandiyar ganganci daga bangaren Direban motar ta Toyota wadda ko lamba babu inda a halin yanzu tuni ya ari karfar kare da hakan ya tabbatar da rashin gaskiyar sa.
Kakakin ya kara da cewa, an mika gawar wadanda suka riga mu gidan zuwa dakin killace gawawwaki dake babban asibitin Odeda, yayin da ake duban lafiyar wadanda suka raunata a asibitin Ijaye dake birnin na Abeokuta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng