‘Yan sandan tawagar Osinbajo sun zane jami’an kwastam a Katsina
A jiya ne jami’an ‘yan sandan tawagar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, sun zane wasu jami’an kwastam uku a Katsina.
Lamarin ya faru ne a kauyen Daddara na karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina inda Osinbajo ya kai ziyara domin jajantawa jama’ar da iftila’in ambaliyar ruwa ta yiwa ta’adi tare da salwantar rayukan mutane fiye da 50.
An samu hatsaniya ne bayan jami’an kwastam sun tsare motar wasu matasa dake dauke da haramtattun kaya da ta fito daga jamhuriyar Nijar.
A yayinda jami’an kwastam din suka tsare motar ne tawagar shugaban kasa ta zo wucewa ta kauyen na Daddara.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewar jami’an kwastam din na kokarin matasan da suka taru a wurin ne amma sai jami’an ‘yan sanda dake tawagar Osinbajo suka yi kuskuren daukan hakan a matsayin wata barazana ga tawagar mataimakin shugaban kasar, saboda jami’an na kwastam na amfani da bindigu domin tarwatsa matasan dake kokarin fin karfinsu domin kwace motar da suka kama.
DUBA WANNAN: Rayukan ‘yan bindiga da ‘yan sanda biyu sun salwanta a wani artabu a hanyar Birin Gwari zuwa Funtua
“Nan da nan ‘yan sandan tawagar mataimakin shugaban kasa suka diro daga motocinsu tare da kokarin kwace bindigogin dake hannun jami’an na kwastan. Bayan kwastam din sun ki basu bindigun ne sai suka fara marinsu da dukansu,” a cewar shaidar.
Shaidar ya kara da cewar, “ganin ana dukan jami’an kwastam din ne sai matasan da suka taru su ma suka fara jifansu da duwatsu. Tuni matasan da aka kama motar su suka arce kafin a gama hayaniyar.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng