'Yan Fashi da Makami sun kar wani Jami'in dan sanda har Lahira a jihar Nasarawa
Wani jami'in dan sanda karkashin reshen hukumar 'yan sanda ta jihar Nasarawa, ya riga mu gidan gaskiya yayin da wasu 'yan fashi da makami suka bindige sa a babbar hanyar Akwanga-Wamba ta jihar.
A ranar Larabar da ta gabata ne kakakin 'yan sanda na jihar ASP Sama'ila Usman, ya bayar da tabbacin wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai a babban birnin jihar na Lafia.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, wannan lamari ya afku ne a ranar 15 ga watan Yuli da ta gabata, inda jami'an na 'yan sanda suka fafata ta hanyar musayar wuta ta harsashan bindiga da 'yan ta'adda.
A sanadiyar wannan bakin gumurzu wani jami'i guda ya raunata sakamakon harbi na harsashin bindiga da aka yi gaggawar garzayawa da shi asibiti kuma daga bisani ya ce ga garin ku nan.
Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar 'yan sanda ta samu nasarar ganin bayan wani ta'adda guda yayin da sauran suka arce da raunuka na harsashen bindiga a tattare da su.
KARANTA KUMA: Boko Haram na sake dandazo a Jihar Borno - Hukumar Soji
A halin yanzu hukumar ta ci gaba da bibiyar sahun wannan 'yan ta'adda inda ta yi nasarar samun wata babbar bindiga kirar Ak47 tare da alburusai masu tarin yawa da 'yan ta'addan suka bari a baya yayin arcewa.
Kazalika kakakin ya nemi al'ummar wannan yanki domin tallafawa hukumar ta 'yan sanda da rahotanni da zasu taimaka wajen cafke wannan miyagu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng