Ambaliyar ruwa ya yi awon gaba da wata Amarya zuwa Nijar daga Katsina
Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren Litinin, 18 ga watan Yuli a jihar Katsina, ya yi ajalin mutane da dama a karamar hukumar Jibia, daga ciki har da wata Amarya, kamar yadda kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Angon Hindatu Yahaya, mai suna Malam Sani Yahaya ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 18 ga watan Yuli, inda yace: “A kauyen Girka na garin Mada-Rumfa dake kasar Nijar aka tsinci gawar Matata.
KU KARANTA: Manyan Sarakunan gargajiya a Najeriya sun gudanar da wani babban taro a Abuja
“Bayan ruwan ya yi awon gaba da gidanmu, sai muka fita muna neman Matata, mun duba cikin baraguzan gine gine da suka fadi ba mu ganta ba, haka zalika mun duba cikin rafuka da fadamai, duk da haka bata nan.
“Ana cikin haka ne sai wasu mutane dake taimaka mana suka kirani daga garin Mada-Rumfa dake kasar Nijar, inda suka ce sun tsinci gawar wata budurwa a cikin wani rafi da ya ratsa ta cikin garinsu, nan da nan muka garzaya Nijar, muka tarar da gawar Matatace.” Inji Ango.
Daga karshe Sani yace a nan suka amshi gawar, suka mayar da ita garin Jibia, sa’annan suka yi mata jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, amma fa yace tun kwanaki uku da suka wuce bai iya cin abinci ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng