Tun bayan dawowarta take haushin karnuka, in ji 'yan uwan wata budurwa da ta je wurin malamin tsibbu

Tun bayan dawowarta take haushin karnuka, in ji 'yan uwan wata budurwa da ta je wurin malamin tsibbu

- Hukumar Yan sanda a Legas ta kama wani malamin tsibbu mai shekaru 23 bisa zarginsa da yiwa wata daliba mai shekaru 29 fyade

- Dan tsibun mai suna Mustapha Hammed, da ake kira Alfa ya yiwa dalibar karyar cewa anyi masa wahayin cewa zata mutu cikin sa’o’i 24

- Ya kuma shaidawa mata cewa za'a iya kawar ta mutuwarta idan ya yi mata wankan tsarki

Hukumar Yan sandan Najeriya reshen jihar Legas ta kama wani dan tsibu mai shekaru 23 mai suna Mustapha Hammed da ake kira “Alfa” bisa zarginsa da yiwa wata dalibar Kwallejin Ilimin Fasaha dake Akoka Legas fyade.

Jaridar Punch ta wallafa cewar Hammed ya fadawa dalibar cewa ya gano cewa zata mutu cikin sa'o'i 24 muddin ba ta amince anyi mata wankan tsarki ba.

Hammed ya ce budurwarsa ta kawo masa dalibar, shi kuma ya kwadaita da son kwanciya da ita bayan ya gane cewar bata taba sanin namiji ba.

Legit.ng ta tattaro cewa an tafi da dalibar unguwar Itowolo dake yankin Ikorodu dake Legas inda za'ayi mata wankan tsarkin.

Tun bayan dawowarta take haushin karnuka, in ji 'yan uwan wata budurwa da ta je wurin malamin tsibbu

Rumfar malamin tsibbu

A yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a ranar Litinin 16 ga watan Yuli, kwamishinan Yan sandan Legas, Edgal Imohimi yace: "Dan tsibun ya yaudari dalibar cewa ya gano zata mutu cikin sa'o'i 24. Ya kaita Ikorodu dake Legas don yi mata wankan tsarki amma yayi mata fyade duk da cewa yarinyar bata taba saduwa da na miji ba.

"Mahaifin yarinyar yace tun bayan afkuwalar lamarin, yarinyar ta fita hayyacin ta kuma tana cikin damuwa game da abinda dan tsibun ya aikata gareta domin ko Magana bata iya yi sai haushin karnuka tun bayan dawowarta."

DUBA WANNAN: Matasa sun fashe kan kwamishinan 'yan sandan jihar Taraba da jifa

Wanda ake tuhumar, dan asalin jihar Oyo, ya amsa cewa shi ne ya kawar wa yarinyar da budurcinta bayan ya sadu da ita a gidansa dake Ikorodu don yi mata wankan tsarki. Saidai y ace da yardarta hakan ya faru tare da bayyana cewar yana son zai aure ta ne.

Kamar yadda kwamishina Yan sandan ya bayyana, a halin yanzu an tura binciken lamarin zuwa sashen kula da jinsi na hukumar don cigaba da bincike. Ya kuma ce za'a gurfanar da wanda ake tuhuma gaban kotu bayan an kammala bincike a kan lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel