Za'a bawa Najeriya bakuncin wasan kwallon kafa na kungiyoyin kwallon kafa na yankin Afrika ta yamma a shekarar 2021

Za'a bawa Najeriya bakuncin wasan kwallon kafa na kungiyoyin kwallon kafa na yankin Afrika ta yamma a shekarar 2021

An tabbatar da kasar Najeriya a matsayin mai masaukin bakin kwallon kafa na yankin Afirka ta yamma wato West African Football Union (WAFU)

Za'a bawa Najeriya bakuncin wasan kwallon kafa na kungiyoyin kwallon kafa na yankin Afrika ta yamma a shekarar 2021

Za'a bawa Najeriya bakuncin wasan kwallon kafa na kungiyoyin kwallon kafa na yankin Afrika ta yamma a shekarar 2021

An tabbatar da kasar Najeriya a matsayin mai masaukin bakin kwallon kafa na yankin Afirka ta yamma wato West African Football Union (WAFU).

Kamar yanda muka samu rahoto a ranar Talatar nan, masu daukar nauyin gasar sunce Najeriya ce zata zamo ta uku a masu masaukin bakin, wanda za'ayi gasar a shekarar 2021.

DUBA WANNAN: Kalli yawan kudaden da suke ajiye a Najeriya wanda har yanzu kotu bata bada damar a taba su ba

Ofishin jakadancin labarai ya ruwaito cewa kasar Senegal ce zata karbi bakuncin masu gasar a watan Satumban shekarar 2019.

Gasar ta WAFU wacce Fox Sports ta dau nauyi, an gabatar da ita a watan Satumbar shekarar 2017 wanda kasar Ghana ta zama mai masaukin baki kuma ta dauki kofin.

WAFU dai ta kunshi kasashe 16 ne, wadanda aka raba su bangarori biyu.

Bangaren farko sune Cape Verde, Gambia, Guinea, Guinea-Bissau, Liberia, Mali, Mauritania, Senegal da Sierra Leone.

Bangaren na biyu ya kunshi Benin, Burkina Faso, Ivory Coast, Ghana, Najeriya, Nijar da Togo

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel