Sojin Najeriya sun kwato garin Yobe da ‘yan Boko Haram suka kwace a hannunsu

Sojin Najeriya sun kwato garin Yobe da ‘yan Boko Haram suka kwace a hannunsu

Hukumar sojin Najeriya ta bayyana cewar dakarunta sun sake kwato garin Jilli na jihar Yobe da ‘yan Boko Haram suka kwace ranar daga hannunsu ranar Asabar da ta gabata.

Da yake Karin haske a kan harin na garin Jilli, kwamandan soji na Ofireshon lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas Roger, ya tabbatar da cewar yanzu haka komai yana karkashin kulawar dakarun soji a yanki da kewayen garin.

Nicholas, ya bayyana harin da cewar abun takaici ne sannan ya kara da cewa faruwar hakan ba sabon abu bane a yanayi na yaki.

A duk inda ‘yan ta’adda suke, tilas a samu nau’in hare-hare daban-daban da suka hada da amfani da sinadarai masu fashewa da ire-irensu.

Sojin Najeriya sun kwato garin Yobe da ‘yan Boko Haram suka kwace a hannunsu
Manjo Janar Nicholas

Abinda ya faru a Jilli ba sabon abu bane a yanayi na aikin soja a yankunan dake fama da hare-haren ‘yan ta’adda,” a cewar Nicholas.

Kwamandan ya amince cewar sojoji n sun mutu yayin harin, saidai bai ambaci adadi ba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun cafke dan takarar gwamnan Borno a wurin taron Atiku a Maiduguri

Zamu samar da bayanai ga kafafen yada labarai dangane da harin garin Jilli, amma dole na sanar da ku cewar aikin soja aiki na tsaro da ba komai ake iya bayyanawa ba saboda wasu dalilai na aiki. Tilas mu tantance bayananmu kafin sakin su ga duniya,” in ji Nicholas.

A ranar Lahadi ne wata kafar yada labarai ta kasar waje ta watsa rahoton cewar sojoji da yawa sun yi batan dabo bayan harin da Boko Haram suka kai garin Jilli. Rahoton da hukumar soji ta karyata tare da bayyana cewar ya saba da ka’idar aikin jarida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel