Cikin Hotuna: Jerin 'yan wasa 5 na Duniya mafi daukar albashi a shekarar 2018
Cikin sabuwar kididdigar da mujallar Forbes ta fitar a bana ya bayyana yadda fitaccen dan kwallon kafar nan na Barcelona watau Lionel Messi, ya yiwa babban abokin adawar sa na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Cristiano Ronaldo fintinkau ta fuskar samu dukumar dukiya a wannan shekara ta 2018.
A shekarar da ta gabata dai Ronaldo shike jan ragamar 'yan kwallon kafa ta samun dukiya da kuma tarin ta, sai dai a halin yanzu Messi ya karbe wannan ragama da zai samu doriya ta shigar dukiya asusun sa har ta kimanin Fan miliyan 2.2.
Kididdigar da mujallar ta Forbes ta fitar dangane da masu sana'ar wasanni da nishadantar da al'umma a duniya ya bayyana yadda fitaccen dan wasan kutofo watau Floyd Mayweather ya ciri tutar wannan jeranto na masu samun dukumar dukiya a bana.
Legit.ng ta kawo muku jerin 'yan wasa biyar na duniya masu sana'ar nishadantar wa da suka yi zarra ta fuskar samun dukiya:
5. Neymar
Sana'a: Kwallon Kafa (Kungiyar PSG)
Dukiya: Fan Miliyan 67.95
4. Conor McGregor
Sana'a: Wasan Kutufo
Dukiya: Fan Miliyan 74.75
3. Cristiano Ronaldo
Sana'a: Kwallon kafa (Kungiyar Juventus)
Dukiya: Fan Miliyan 81.54
KARANTA KUMA: Jihar Kebbi na samar da Tan 3.6m cikin Tan 5.7m na Shinkafa da Najeriya ke bukata a duk shekara
2. Lionel Messi
Sana'a: Kwallon kafa (Kungiyar Barcelona)
Dukiya: Fan Miliyan 83.81
1. Floyd Mayweather
Sana'a: Wasan Kutufo
Dukiya: Fan Miliyan 207.6
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng