Ronaldo yayi furuci bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

Ronaldo yayi furuci bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

A ranar Litinin din da ta gabata ne fitaccen dan wasan nan na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake kasar Andalus watau Cristiano Ronaldo, ya kamalla sauya sheka zuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake kasar Italiya.

A yayin gabatar da mashahurin dan wasan ga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Juventus dake birnin Turin a kasar ta Italiya, Ronaldo ya bayyana cewa kada su damu da kwana biyun da ya yi a duniya kasancewar sa mai shekaru 33 a duniya.

Yake cewa, shi a nasa hangen kungiyar ta Juventus tana daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafi zakakuranci da kyawu a duniya, inda ya ce ya yanke wannan shawara ta sauya sheka sakamakon tuntube na abokan arziki da kuma abokan sa na sana'a da suke ganin dacewar sa da kungiyar ta Juventus.

Legit.ng ta fahimci cewa, mafi akasarin kwallon kafa tauraruwar su na disashewa yayin da suka doshi shekaru 30 da haihuwa a duniya, inda suke barin manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya zuwa wasu kungiyoyin dake nahiyyar Asia da kuma yankin kasashen Larabawa.

Ronaldo yayi furuci bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid
Ronaldo yayi furuci bayan barin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid

Sai dai ko shakka babu Ronaldo ya bayyana cewa, har yanzu na jin yarinta a tattare da shi da ya sanya ya yanke hukuncin sauya sheka zuwa kungiyar ta Juventus sabanin yadda wasu fitattun 'yan kwallon kafa da suka kai shekaru irin nasa ke sauya sheka zuwa wasu kungiyoyin kwallon kafa dake Qatar, Amurka, Sin da sauran kasashe na Larabawa.

Ronaldo ya ci gaba da cewa, kasancewar girma da daukakar kungiyar kwallon kafa ta Juventus ya sanya ya yanke wannan shawara gami da kudirin da ta sanya a gaba da kuma sabo na samun nasara a kowace shekara.

KARANTA KUMA: Matakai 10 da shugaba Buhari ya dauka dangane da Kashe-Kashe a kasar nan - Fadar Shugaban Kasa

Fitaccen dan wasan ya kuma yabawa mai horas da 'yan wasa na kungiyar, Max Allegri da kuma shugaban ta baki daya, Andrea Agnelli, da suka ba shi dama ta shigowa wannan babbar kungiya.

Ya kara da cewa, shekaru 9 da ya shafe a kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasance abun soyuwa a gare sa, inda yake mika sakon sa na godiya tun daga karkashin zuciya tare da ba su hakurin wannan sabon kalubale da ya sanya gaba a rayuwar sa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel