An bayar da kiyasin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Katsina

An bayar da kiyasin mutanen da suka mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Katsina

Mutane 49 ne suka mutu wasu 20 kuma sun bata sakamakon ambaliyar ruwa data afku bayan an kwarara ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu kauyuka dake iyakar Katsina da Jamhuriyar Nijar kamar yadda hukumar bayar da Adaji ta bayyana a yau Talata.

Kauyuka biyar ne ambaliyar ruwar ta shafa bayan wata rafi tayi ambaliya bayan ruwan saman da aka kwana ana yi a daren Lahadi, inji Aminu Waziri shugaban hukumar agaji na jihar Katsina KSEMA.

A cewarsa, jami'an hukumar sun gano gawawaki 49 daga kauyukan biyar kuma har ila yau ana neman wasu mutane 20 da har yanzu ba'a gano inda suke ba.

Ambaliyar ruwa a Katsina: An bayar da kiyasin mutanen da suka rasa rayyukansu

Ambaliyar ruwa a Katsina: An bayar da kiyasin mutanen da suka rasa rayyukansu

DUBA WANNAN: Karyar walwalar ciki ta kare tunda 'Fayose' ya fadi zabe - Farfesa Sagay

An tsinto gawar mutane 24 a kauyukan Mada Rumfa da Kantumi da ke makwabtaka da Jamhuriyar Nijar.

"An zakulo wasu gawawakin ne daga ginin da ya rushe a kansa sakamakon ambaliyar ruwan," inji Waziri.

Sama da mutane 2,000 da suka rasa muhallinsu suna zaune ne a makarantun frimari da ke Jibia, yayin da wadanda suka sami raunuka kuma suna asibiti inda ake jinyarsu.

"Gwamnatin jihar ta samar da kayayakin tallafi ga wadanda abin ya shafa kuma muna kira da hukumar bayar da agaji na kasa NEMA da ta taimakawa wadanda abin ya shafa."

Ana samun ambaliyar ruwa a sassan Najeriya daban-daban musamman lokacin damina daga watannin Mayu zuwa Satumba.

A ranar Talata, an samu sanarwa a gidan radiyo na jihar cewa masu hasashen yanayi sunyi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a sassan kasar nan saboda yanayin ruwan sama da ake samu ya karu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel