Matashiya yar Najeriya da aka zarga da kwace saurayin kawarta ta mutu (hotuna)
Ba sabon labari bane cewa wasu mata sun kware wajen kwace mazaje da samarin kawayensu. Suna aikata hakan ba tare da tsoron abun da ka iya zuwa ya dawo dare su ko kawayen nasu ba.
Yanzun nan aka kawo rahoton cewa wata matashiya da ta kwace saurayin kawarta da aka yi masu baiko, Junaidu Usman Abubakar ta rasu. Yar wasar Kannywood Aisha Humairah (@ayshatulhumairah) ce ta sanar da mutuwar Farida Bashir Ikara a shafinta na Instagram.
Humairah ta bayyana cewa Ikara ta rasu bayan ta kama korafin ciwon ciki.
Kalli rubutun Humairah:
An tattaro cewa a shekarar 2017, aminiyar Ikara, Aisha (@ayeesha_oc), ta je shafinta na Instagram ta bayyana yadda ta kwace mata saurayinta da aka yi masu baiko bayan ta taya ta tsara yadda shirye-shiryen auranta zai kasance.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng