2019: Atiku ya nemi goyon bayan gwamna Dankwambo na Gwambe

2019: Atiku ya nemi goyon bayan gwamna Dankwambo na Gwambe

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi goyon bayan gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

- Atiku yayi alkawarin kawowa jihar cigaba masu dinbin yawa

2019: Atiku ya nemi bayan gwamna Dankwambo

2019: Atiku ya nemi bayan gwamna Dankwambo

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya nemi goyon bayan gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo, domin ya bashi hadin kai wurin cimma burinsa na lashe kujerar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

DUBA WANNAN: An tura jami'an tsaro yankin da 'yan fashi suka yi barazanar kai hari a jihar Lagos

Atiku yayi kiran a lokacin da ya kaiwa gwamnan jihar ziyara a Gombe ranar Litinin dinnan. Yace akwai bukatar su hade kai domin hakan shine zai basu nasarar lashe zaben shekarar 2019.

Atiku yayi alkawarin kawowa jihar cigaba masu dinbin yawa.

"Domin kawo mutanen mu cigaba ya kamata mu hade kawunan mu, mutukar mun damu da cigaban wannan kasar tamu hakan shine zai kawo mana canjin da muke bukata," inji shi.

Da yake nashi jawabin, Dankwambo ya bukaci Atiku daya baiwa mutane kwarin guiwa, ta hanyar kawo cigaba ga jam'iyyar PDP, da kuma shirye - shiryen zaben shekarar 2019.

A cewar shi, siyasa tana bukatar karfafawa mutane guiwa domin samun karfin guiwar su shine zai basu damar zaben wannan jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel