Zaben Ekiti: Obasanjo ya sake rubuta zungureriyar wasika
Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya rangadawa sabon zababben gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, wasikar taya shi murnar yin nasara a zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi ranar Asabar, 14 ga watan Yuli, da ta gabata.
Obasanjo ya ja hankalin Fayemi tare da bashi shawarar ya dauki nasarar da ya samu a matsayin wani nauyi da mutanen jihar Ekiti suka dora a wuyansa.
Jam’iyyar PDP tayi watsi da sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar na zaben gwamnan jihar Ekiti da aka yi jiya.
A sakamakon da INEC ta fitar, dan takarar jam’iyyar APC, Kayode Fayemi, ya sami nasara a kan dan takarar PDP, Farfesa Kolapo Olusola.
DUBA WANNAN: Fadar shugaban kasa ta bayyana sirrin nasarar APC a zaben Ekiti
Da sanyin safiyar jiya, Lahadi, ne hukumar INEC ta sanar da cewar Fayemi na APC ya samu nasara a kananan hukumomi 11 a cikin 16 dake jihar ta Ekiti. Fayemi ya samu jimillar kuri’u 197,459 yayinda Kolapo ya samu kuri’u 178,121.
Saidai a jawabin da ta fitar ta bakin kakakinta, Kola Ologbondian, ta bayyana cewar an yi masu fashin zabe da tsakar rana tare da yin watsi da sakamakon zaben gabadayansa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng