Kwankwaso ya cire jar hula, duba hotunansa
A ranar juma'a da ta gabata ne wasu hotunan tsohon gwamnan Kano kuma sanata mai ci, Rabi'u Musa Kwankwaso, suka fantsama a dandalin sada zumunta daban-daban inda aka hange shi a cikin wata Coci ba tare da jar hularsa sanye a kansa ba.
Abu biyu da suka bawa jama'ar dake yawo da hotunan na Kwankwaso a dandalin sada zumunta sune; ganin shi babu jar hula da kowa ya san shi da ita da kuma kasancewarsa a a Coci a ranar juma'a da Musulmi ke zuwa masallaci.
DUBA WANNAN: Abu 4 da PDP zata yi domin dawo da martabarta a Najeriya
Ganin Kwankwaso a Coci ba wani abun mamaki bane idan aka yi la'akari da kasancewarsa shugaba kuma mai burin zama shugaban kasar Najeriya dake da yawan mabiya addinin Kirista.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng