Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau

Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau

- Yau ce ranar karshe a gasar cin kofin Duniya da ake gudanarwa a kasar Rasha

- An cire duk kasashen saura biyu kacal da zasu kara a wasan karshe

- Ba a taba haduwa a wasan karshe na cin kofin duniya tsakanin kasashen biyu ba

Yau da misalin karfe 4 na yamma kasashe Faransa da Croatia za su kara a wasan karshen na gasar cin kofin duniya.

Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau
Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau

Tarihin haduwar Faransa da Croatia

Masu hasashe da dama na ganin kasar Faransa ce ta lashe gasar, duba da irin ‘yan wasan da take da su da kuma tarihin da ta kafa a wannan gasa ta cin kofin duniya.

Faransa ta doke Croatia ne a shekarar 1998, 1999 da kuma shekarar 2000, sai kuma canjaras da aka shi ma har guda biyu a shekarar 2004 da 2011. Faransa ta kasance tana da tarihin samun nasara akan kasar Croatia.

Kwazon ‘yan wasa

Masu hasashe daban daban na ganin wannan nasara za tayi tasiri musamman idan aka yi duba da yadda ‘yan wasan kasar Faransa ke nuna hazaka, kamar irin su Antoine Griezmann wanda yana da kwallaye 3 a gasar, sai kuma Kyllian Mbappe shi ma yana da kwallaye 3.

Dalilai 2 da yasa Faransa zata yi nasara a wasan karshe na kofin duniya yau
Kofin kwallon kafa na duniya

Wadanan yan wasa dai suna cigaba da nuna bajinta, sannan ana ganin zasu iya taimakawa kasar ta Faransa wajen lashe wannan kofi. ‘Yan wasan dai sun zamo jigo a Faransa wajen yiwa kungiyar jagoranci a wasanni da dama da suka wuce.

KU KARANTA: Wata budurwa a kasar Saudiyya zata shafe shekaru 2 gidan yari saboda rungumar mawaki a gidan rawa

A bangaren kasar Croatia kuwa, ita ma ba a barta a baya ba

Amma duk da wannan hasashe da aka yi akan kasar Faransa, ita ma kungiyar kwallon kafa ta Croatia ba a barta a baya ba, musamman idan aka yi duba da irin kwazo da kokari na shugaban ‘yan wasan kungiyar wato Luka Modric yake a gasar, wannan dan wasan ya kasance jigo wajen kawowa kungiya ta Croatia har zuwa wasan karshe na gasar cin kofin duniyar.

Bayan nan akwai yan wasa kamar Ivan Rakitic, Rebic da Mario Mandzukic duk suma ana ganin kokarinsu da suka nuna a wasannin da kasar ta yi a baya zai taimaka mata wajen ganin ta kafa sabon tarihi.

Amma ko mene ne yau da misalin karfe 4 na yamma wadannan kasashe zasu kara, sannan kowa zai sa ido domin ganin irin sakamakon da zai biyo baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel