Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

A yau, Asabar, 14 ga watan Yuli, dubun dubatar mutanen jihar Ekiti suka fito a mazabunsu dake fadin jihar domin kada kuri’unsu a zaben gwamna.

Takarar kujerar gwamnan za a iya cewa tsakanin jam’iyyu biyu ne; PDP mai mulkin jihar da kuma APC mai mulkin kasa.

Jam’iyyar PDP ta tsayar da Farfesa Kolapo Olusola, mataimaki ga gwamnan jihar Ayodele Fayose, yayinda jam’iyyar APC ta tsayar da Kayode Fayemi, ministan Buhari na albarkatun kasa kuma tsohon gwamnan jihar daga shekarar 2010 zuwa 2014.

Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Mutane 667,028 ne hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana cewar zasu kada kuri’a zaben, kamar yadda baturen zabe a jihar, Farfesa Abdulganiy Olayinka, ya sanar.

DUBA WANNAN: Zaben Ekiti: Matsaloli uku da kan iya kayar da PDP wan-war a zaben gobe

Saidai a yayinda ko kuri’u ba a kamala kadawa ba, sai gashi magoya bayan gwamnan jihar Fayose sun fito kan titi a Ado-Ekiti, babban birnin jihar ta Ekiti, inda suke tikar rawa suna waka tare da fadin cewar, “Ekiti ta Fayose ce, kudi ba zai saye mu ba”.

Har yanzu dai ba a soma tattara sakamakon zabe a kananan hukumomi ba balle a kai ga matakin jiha.

Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Magoya bayan Fayose

Zaben Ekiti: Kalli hotunan murnar magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Magoya bayan Fayose bayan sun yi ikirarin hango kyallin nasara

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel