Soji sun kamo masu sayar wa da Boko Haram 'kayan aiki'
Dakarun sojin Najeriya na Operation Lafiya Dole bataliya ta 159 sunyi nasarar damke wasu da ake zargin masu sayar wa 'yan Boko Haram man fetur ne a karamar hukumar Yusufari dake jihar Yobe bayan sun sami bayyanan sirri akan ayyukan dilalan man.
Sanarwar data fito daga bakin Kakakin hukumar sojin, Brig. Janar Texas Chukwu, tace an kama mutanen biyu ne yayin da suke sayan man fetur cikin jarkoki a wata gidan mai mallakar wani dan majalisar jihar Yobe.
Kazalika, Sojin sun kama manajan gidan man tare da masu sayar da man kuma a halin yanzu suna tsare suna amsa tambayoyi sai dai direban tankar ya tsere.
A halin yanzu, jami'an sojin sun bazama cikin gari domin zakulo direban babbar motan da ya gudu.
DUBA WANNAN: Yadda wani dan shekaru 17 ya tsira daga gidan matsafa a Kano
Da haka ne hukumar sojin ta sake kira ga al'umma su rika sanya idanu kan abubuwan dake faruwa a unguwaninsu kuma su kai kara zuwa ofishin hukuma mafi kusa dasu domin a dauki matakin gaggawa.
A wata rohton, Legit.ng ta kawo muku cewa jami'an Yan sanda sun kama wani yaro da ya halaka mahaifinsa a kauyen Pissa, a karamar hukumar Borgu, ta jihar Neja.
An kamo yaron mai suna Abubakar Turuwa wanda ya kashe mahaifinsa Turuwa Ibrahim, bayan da uban wai ya ki yi masa adalci kan rabon shanaye tsakaninsa da dan-uwa nai.
Kwamishinan Yan sandar jihar, Mista Dibal Yakari, yace Saurayin, ya aikata laifin ne da adda inda ya kaftawa uban a ka, wadda hakan ya yanke jini har ajali yayi halin nasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng