Juyin Zamani: Mun kamo dan nan da ya kashe uba nai - Yansanda
- Wai ya kashe uban ne saboda yayi masa rashin adalci kan rabon Nagge
- Ya amsa gaban yansanda cewa yayi laifin
- Za'a maka shi gaban kotu don bin bahasi
A kauyen Pissa, a karamar hukumar Borgu, ta jihar Neja, an samu sa'ar kamo yaron nan Abubakar Turuwa wanda ya kashe mahaifinsa Turuwa Ibrahim, bayan da uban wai ya ki yi masa adalci kan rabon shanaye tsakaninsa da dan-uwa nai.
Kwamishinan yansandar jihar, Mista Dibal Yakari, yace Saurayin, ya aikata laifin ne da adda inda ya kaftawa uban a ka, wadda hakan ya yanke jini har ajali yayi halin nasa.
Kwamishinan, yace saurayin ya amsa laifi nai, kuma zasu mika shi ga kotu domin hukunci.
DUBA WANNAN: Ana taunawa kan dan takara a PDP a Otta
Hukumar yansanda ta ce lallai ya kamata a sanya ido kan ababe da ke faruwa a yankuna don kai rahoton gaggawa domin daukar mataki kafin lamari ya rincabe.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng