Yaki da sata: Yadda ‘Yan Majalisa su ka hana Shugaba Buhari cika alkawarin da ya dauka
Bisa dukkan alamu dai ba a shafi guda ake tafiya tsakanin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ‘Yan Majalisar kasar ba musamman wajen yaki da satar dukiyar kasa wanda yana cikin manyan muradun Shugaban.
Akwai dalilai da dama da su ka sa mu ke ganin Majalisa na cikin masu hana ruwa gudu wajen yakar satar dukiyar kasa da maganin barayi. Daga cikin wadannan dalilai akwai:
1. Tantance Ibrahim Magu
Har gobe dai Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu yana aiki ne a matsayin Mukaddashi bayan da Majalisar har fiye da sau 1 ta ki tabbatar da shi. Majalisar Dattawan tace akwai rahoton da ya nuna cewa Magu bai cancanci ofishin ba.
2. Kudirin safarar kudin sata
Akwai kudirin da Shugaban kasa Buhari ya kawo gaban Majalisa tun a 2016 wanda har yau Majalisar ba tace komai ba. Kudirin zai taimaka wajen yaki da masu safara kudin sata musamman ‘yan siyasan kasar da ke kokarin kai kudi zuwa waje.
3. Kudirin da zai taimaka wajen karbo kudin sata
Haka kuma akwai wani kudirin da zai taimakawa Najeriya wajen karbo kudin sata da aka ajiye a kasashen waje. Wannan kudiri zai taimaka wajen yakan barayi kuma zai dawowa kasar da martabar ta. Sai dai har yanzu Majalisa tayi gum.
4. Doka mai iko na karbe dukiyar sata
Akwai dokar da Shugaban kasa Buhari ya rattaba hannu kan ta wanda ta ba Gwamnati cikakkiyar iko na karbe dukiyar da ake zargi ya hanyar sata aka same ta. Yanzu dai akwai alamun Yan Majalisar Tarayya za su yi fito-na-fito da Shugaban kasar kan wannan kudiri.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng