Ko za'a dawowa Najeriya dukkan dukoyoyinta dake kasashen waje?

Ko za'a dawowa Najeriya dukkan dukoyoyinta dake kasashen waje?

- Zuwan Turawa a qarni na 19 ya kawo wa yankin bakake naqasu

- An kwashi arziki an kai kasashen waje an ajje

- Ana samun kudaden shiga sosai da wadannan kudade

Ko za'a dawowa Najeriya dukkan dukoyoyinta dake kasashen waje?
Ko za'a dawowa Najeriya dukkan dukoyoyinta dake kasashen waje?

A karshen qarni na 19 ne Turawan Ingila suka fara shigowa yankunan da a yanzu ake kira kudancin Najeriya, a wancan lokacin kuwa, ake kiransu kurmi, inda kabilu kan rayu cikin dawa ba ruwasu da wasu,, wanda hakan ke kawo yawan yake-yake.

A shekarar 1897, sojin kasar Ingila suka arma birni mai dumbin Tarihi na Benin, a Edo ta yanzu, kuma sun kwashe kayan tarihi da yawa sun aika Ingila bayan da suka ci ta da yaki.

Cikin ababen da suka dauka harda gunkin nan mai farin jini watau Iyoba (Uwa-Sarauniya).

DUBA WANNAN: Zamu raba muku kudin Abacha gida-gida

A yanzu dai kayayyakin suna Ingila da wasu kasashen inda ake nuna su a gidajen tarihi ake kuma samun kudin shiga dasu.

Wasu na ganin lokaci yayi da za'a maidawa masarautu irin wadannan kayayyaki masu daraja daga sassan Najeriya.

Wasu kuwa na ganin mu bakake bamu ma san darajarsu ba, kuma rigingimunmu ka'iya watsa su cikin shirgi garin yaki ko kone-kone, koma gobara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel