Yanzu-yanzu: Wani dan sanda yayi asarar mazakutarsa

Yanzu-yanzu: Wani dan sanda yayi asarar mazakutarsa

- Rana ta baci ga wani dan sanda mai aikata masha'a da yara maza

- Sakamakon gajiya da halayyar tasa ne mazauna yankin suka zirya masa gadar zare

- Yanzu haka yana can asibiti yan karbar magani

Bala'i ya afkawa wani sufeton dan sanda da ya kware wajen lalata da ‘ya’ya maza (Luwadi) a yau a garin Faskiri na jihar Katsina.

Yanzu-yanzu: Wani dan san yayi asarar mazakutarsa
Yanzu-yanzu: Wani dan san yayi asarar mazakutarsa

Bayanai dai sun tabbatar da cewa a lokacin abin ya faru yana tsaka da aikata masha'ar ne da wani yaro dan shekara 13.

Dama dai tuni mazauna yankin suka gaji da wannan mummunar halayya ta jami’ain dan sandan ta haikewa yara a unguwar, a don haka ne aka shirya masa gadar zare kuma ya hau ta rufta da shi.

KU KARANTA: Karar kwana ta kai wani saurayi gamuwa da budurwar da ya hadu da ita a waya

An garzaya da dan sandan asibiti mafi kusa tare da mazakutar tasa cikin jini rabe-rabe, inda daga bisani kuma aka mayar da shi wani asibitin domin cigaba da karbar magani.

Har ya zuwa yanzu da muke kawo muku wannan rahoto ba bayyana sunan jami’ain ba. Kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito.

Da zarar an samu cikakkun bayanai kan labarin zamu kawo muku……

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng