Yadda wani basaraken Jihar Zamfara ya yi wata gagarumar sadaukarwa domin kare jama'ar sa

Yadda wani basaraken Jihar Zamfara ya yi wata gagarumar sadaukarwa domin kare jama'ar sa

A lokacin da 'yan bindiga suka iso kauyen Kucheri dake karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara a ranar 6 ga watan Yuli, sun tarar da hakimin kauyen, Ibrahim Madawaki, yana ganawa da talakawarsa a fada bayan kammala sala.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Yan bindigar sun iso kauyen a kan babura suna harba bindiga sama don sanar da isowarsu.

Bayan sun mamaye kauyen, 'yan bindigar sun bukaci hakimin kauyen ya bayyana kansa, bayan ya fito sai suka umurce shi ya hau babur su tafi dashi amma sai ya ki hawa inda ya kada baki ya tambaye su shin wane laifi ya yi musu da zasu yi masa hakan.

Mutuwar ban tausayi: Yadda Hakimi ya rasa ransa a kokarinsa na kare talakawansa

Mutuwar ban tausayi: Yadda Hakimi ya rasa ransa a kokarinsa na kare talakawansa

KU KARANTA: Ai shugaba Buhari ba zai sanya ayi kashe-kashe ba - Gowon

Da suka lura dai ba zai bi umurninsu ba sai dayansu ya buge shi da gora, daga nan sa hakimin ya ce dasu, "Ina rokon ku idan kun kashe ni, kar ku taba kowa daga cikin mutane na."

Yadda wani basaraken Jihar Zamfara ya yi wata gagarumar sadaukarwa domin kare jama'ar sa

Yadda wani basaraken Jihar Zamfara ya yi wata gagarumar sadaukarwa domin kare jama'ar sa

Daga nan fa sai 'yan bindigan suka bude masa wuta har sai dai Madawaki ya dena numfashi amma basu taba kowa a garin ba kamar yadda ya roke su kafin su kashe shi.

Wani daga cikin iyalan marigayi Madawaki ya shaidawa TheCable cewa 'yan bindigan sun harbi Madawaki har sau bakwai a kansa.

"Basu bar wajen ba sai da suka tabbatar ya mutu. Sannan suka haye baburansu suka koma dajin da suke zama wanda ke kusa da kauyen, inji shi.

Madawaki ya rasu yana da shekaru 63 a duniya, ya rasu ya bar mata hudu da yara 34. Mutane suna ta zuwa fadan shugaban marigayin don yin ta'aziyya.

Duk da cewa 'yan bindaigan sun saba kashe mutane a kauyen, kashe mai unguwar Kucheri ya jefa tsoro cikin zukatan mutanen Kucheri inda kowa ke jimamin abinda ka iya faruwa idan yan bindigan suka dawo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel