Ai shugaba Buhari ba zai sanya ayi kashe-kashe ba - Gowon

Ai shugaba Buhari ba zai sanya ayi kashe-kashe ba - Gowon

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Janar Yakubu Gowon mai murabus yace rashin adalci ne yasa ake zargin shugaba Muhammadu Buhari da gazawa cikin rikicin makiyaya da manoma a dadalin sada zumunta.

Gowon yayi wannan maganar ne jiya a Filato yayin da ya kaiwa Gwamna Simon Lalong ziyarar ta'aziyya bisa kashe-kashen da akayi a wasu kauyuka dake karamar hukumar Barikin Ladi.

Tsohon shugaban kasar yace babu yadda za'ayi wani shugaban kasa ya goyi bayan kashe mutanensa, ya kuma koka kan yadda aka saki wasu daga cikin wadanda aka samu cikin kashe-kashen bayan an tafi dasu Abuja.

Buhari da na sani ba zai taba goyon bayan kashe-kashe ba - Gowon
Buhari da na sani ba zai taba goyon bayan kashe-kashe ba - Gowon

DUBA WANNAN: Wani dattijo mai shekaru 60 ya maka wata budurwa a kotu saboda taki aurensa

Gowon wanda shine Ciyaman din Kungiyar addu'a na Najeriya ya bayar da shawarar cewa a gudanar da bincike kuma a hukunta wadanda aka samu da hannu cikin kashe-kashen a nan jihar Filato da aka aikata laifin.

A jawabinsa, Gwamna Lalong yace gwamnatin jihar tana gab da saka hannu kan dokar da zata bawa gwamnatin jihar daman hukunta wanda dukkan wanda aka samu da laifi a jihar ba tare da an kaisu Abuja ba.

Ya kuma yabawa tsohon shugaban kasar kan yadda yake kulawa da jihar a matsayinsa na Uban kasa tare da alkawarin aiki tukuru don ganin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya samu a jihar.

Gwamnan ya dau alwashin ganin cewa an samu dawamamen zaman lafiya a jihar.

Cikin wanda suka tarbi tsohon shugaban kasar har da mataimakin gwamna, farfesa Sonni Tyodden da mambobin kwamitin tsaro na jihar wanda suka hada da sakataren gwamnan jihar, Cif Rufus Bature da shugaban ma'aikatan jihar John Dafaan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel